Fasa-kwauri na shafar tattalin arzikin kasa – Hukumar Kwastam

0 617

Hukumar Kwastam ta jihar Kano da Jigawa ta tara sama da Naira biliyan 18 a matsayin kudaden shiga daga watan Janairu zuwa Yuni.

Kwanturola na yankin Sambo Dangadima, ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi a Kano ranar yau Laraba.

Ya ce hukumar ta bayar da umarnin tura jami’anta zuwa kan iyakokin kasar nan domin kara kaimi wajen dakile duk wani nau’in fasa-kwauri.

Dangadima ya nemi goyon bayan sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki wajen wayar da kan jama’a kan illar fasa-kwauri wanda hakan ke shafar tattalin arzikin kasa. Ya kuma nemi goyon bayan masu ruwa da tsaki wajen wayar da kan jama’a don gujewa fasa-kwaurin da kuma rungumar hanyoyin shigo da kayayyaki da kuma fitar da su ta hanyar da doka ta amince.

Leave a Reply

%d bloggers like this: