An tsare wani mutum bisa zargin yin lalata da matar makwabcinsa

0 418

Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare wani mutum da ya bukaci a sakaya sunan sa daga unguwar Dorayi da ke karamar Hukumar Gwale ta Jihar bisa zarginsa da yin lalata da matar makwabcinsa.

An zargi mutumin da laifin fita tare da matar zuwa wani wuri a duk lokacin da mijinta ba ya kusa.

Mai shigar da kara ya shaida wa kotun cewa bayan ya lura da alakar matarsa da wanda ake tuhuma sai mijin ya sake ta.

Ya ce bayan rabuwar auren; sai dai wanda ake zargin ya bai wa matar daki a gidansa domin ta ajiye kayanta, lamarin da ya sa tsohon mijin ya kai rahoto ga ‘yan sanda.

Wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin. Khadi, Sani Tanimu Sani Hausawa, bayan ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake tuhumar, ya ce za a iya bayar da belin wanda ake kara idan ya kawo wanda zai tsaya masa, kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Yulin 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: