A wani labarin kuma Cibiyar Gargadi ta Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya (FEW Centre) ta sake fitar da sanarwar gargadin ambaliyar ruwa ga Adamawa da wasu jihohi takwas na Arewa.
Wata takardar da ke dauke da sa hannun Darakta mai kula da zaizayar kasa da ambaliyar ruwa, Usman Abdullahi Bokani, ya fitar a Abuja ranar Litinin, ta bayyana cewa akwai yiwuwar wasu jahohin Arewa za su fuskanci ruwan sama mai karfin gaske wanda zai iya haifar da ambaliya a tsakanin ranakun 25 zuwa 29 ga watan Agustan 2025.
Bokani, wanda ya yi kira ga ma’aikatansa da ke cibiyoyin ma’aikar a jihohin da abun ya shafa da su bayar da rahoto kan duk wani sauyin yanayi a jihohinsu, ya kuma bayyana cewa, jihohin Bauchi, Gombe, Jigawa, Kano da Katsina, na kan gaba-gaba kan yiwuwar Afkuwar ambaliyar.