Firaiminstan Chadi ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin ƙasar

0 178

Firaiminstan Chadi wanda gwamnatin sojin ƙasar ta bai wa muƙamin, Succès Masra ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin ƙasar, mako guda bayan shugaban mulkin sojin ƙasar, Mahamat Déby ya sanar da tasa aniyar.

Mista Masra, tsohon madugun ƴan’adawa ya sanya hannu a yarjejeniyar sulhu da shugaba Deby bayan ya koma ƙasar daga gudun hijira, kafin daga bisani a bashi matsayin firaiminista a watan Janairu.

Masra ya shaida wa magoya bayansa a wani taron gangamin da aka yi a jiya Lahadi cewa, zai tsaya takarar shugabancin ƙasar ne saboda ya haɗa kan jama’a tare da kawo musu sauƙi.

Sai dai ƴan’adawa sun soki matakin da cewa wani makirci ne aka ƙulla domin nuna wa jama’a cewa shugaba Deby na da abokan hamayya, alhali Deby na da yaƙinin lashe zaɓen.

Babban abokin hamayyar Deby, kuma jaroran ƴan’adawa, Yaya Dillo an kashe shi a wata musayar wuta da jami’an tsaro a ranar 28 Fabairu.

Gwamnatin ƙasar ta ɗora laifin harin a kansa, lamarin da ya musanta. Shugaba Déby ya karɓi ragamar shugabancin ƙasar ne bayan kisan mahaifinsa da ƴantawaye suka yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: