Fiye da mutum 54 ne suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata bayan da babbar motar da suke ciki ta kife a kudancin kasar Mexico

0 38

Akalla mutane 54 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata bayan da babbar motar da suke ciki ta kife a kudancin kasar Mexico.

Fiye da mutane 150 da aka ce bakin haure ne daga tsakiyar nahiyar Amurka, sun makale a cikin tirelar motar a lokacin da ta kife a kasa.

Hotunan da aka yada sun nuna wadanda abin ya shafa sun bazu a kan titin da ke kusa da motar da ta kife.

Sabina Lopez, wacce ke zaune a kusa da wajen wacce ta ruga a guje zuwa wajen bayan hadarin, ta shaidawa manema labarai cewa ta ga mutane da dama na kukan ciwo, wasu sun makale a cikin motar, wasu kuma a sume.

Mazauna yankin sun bai wa wadanda suka tsira ruwan sha da wayoyin hannu don kiran ‘yan uwansa. Sun kuma ce direban da wani mutum da ke tare da shi sun ji rauni, amma sai suka gudu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: