

- Gwamna Zulum ya raba wa likitoci fiye da 80 didaje da kudi Naira miliyan 79 don inganta rayuwarsu - July 2, 2022
- Manyan Sarakunan kasar Yarabawa sunyi kiran samun zaman lafiya daga gwamnati kafin zaben 2023 - July 2, 2022
- Kasar Jamus za ta fara dawo wa da Najeriya dubban kayayyakin tarihin ta da aka wawushe tun lokacin mulkin mallaka - July 2, 2022
Gamayyar dakarun tsaro a jihar Neja sun kashe mutane 100 da ake zargin ‘yan fashin daji ne a wani aiki da suka gudanar a kauyen Bangi dake karamar hukumar Mariga ta jihar.
Kwamishinan ‘yansanda na jihar, Bala Kuryas, ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa yau a Minna.
Bala Kuryasa wanda yace dakarun tsaron sun kwato babura 61 daga hannun ‘yan fashin dajin lokacin aikin da aka yi a jiya, yace wasu daga cikinsu sun tsere da raunin harbin bindiga.
Kazalika, gwamnatin jihar Neja ta yabawa dakarun tsaron bisa nuna kwarewa yayin musayar wuta tsakaninsu da ‘yan fashin daji.
Shugaban kwamitin tsaro na karta kwana kuma kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu, Emmanuel Umaru, shine yayi yabon.
Kwamishinan ya tabbatar da mutuwar wani jami’in tsaro daya yayin aikin.