Jamiar Tarayya dake Dutse tace ta sayi Kimanin littafai 500 da mujallu 1000 wanda kudinsu ya kai naira miliyan 100 da nufin bunkasa karatun dalibai

0 89

Jamiar Tarayya dake Dutse tace ta sayi Kimanin littafai 500 da mujallu 1000 wanda kudinsu ya kai naira miliyan 100 da nufin bunkasa karatun dalibai a jami’ar, bugu da kari jamiar ta kuma kammala duk wasu shirye-shirye domin karba da gudanar da asibitin Rasheed Shokini wanda zai kasance asibitin koyarwa na jami’ar.

Mataimakin Shugaban jami’ar Farfesa Abdulkadir Muhammad Sabo ne ya bayyana yayin taron manema labaran daya kira a jiya don bayyana irin nasarorin daya cimma bayan karbar ragamar jagorancin jami’ar tsawon shekara guda. Yace jami’ar ta sami nasarar biyan dukkanin bassusukan da ma’aikatan jamiar ke bin ta.

Wakilinmu na Dutse Zulkiflu Abdallah Dagu ya kasance a wajen taron manema labaran ga kuma rahotan daya hada mana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: