‘Yan fashin daji sun raba mutane kimanin dubu 15 ga muhallansu a kauyuka 8 dake karamar hukumar Sakaba a jihar Kebbi

0 35

‘Yan fashin daji sun raba mutane kimanin dubu 15 ga muhallansu a kauyuka 8 dake karamar hukumar Sakaba a masarautar Zuru ta jihar Kebbi.

An rawaito cewa ‘yan fashin dajin sun mamaye kauyen ta hanyar kakagida a gidajen da babu kowa inda suke cin abincin da masu gidajen suka gudu suka bari.

Kauyukan dake hannun ‘yan fashin daji a gundumar Makuku sun hada da Makuku, Doka, Jigawa, Mahuta, Kurmin Hudo, Bien, Sakaba da Maroro.

Gundumar Makuku tana bangaren kudancin masarautar Zuru da tayi iyaka da jihar Neja kuma tana da dazuka da tsaunuka wadanda ‘yan fashin dajin ke amfani domin buya da kuma samun zuwa masarautar Yauri dake makotaka.

Wani jigon al’umma, Alhaji Auwal Makuku, yace an aika da wasu sojoji zuwa kauyukan Ayyu da Dankolo, wadanda suka taimaka sosai wajen dakile bazuwar ‘yan fashin dajin, ba dan haka ba da tuni sun isa garin Zuru.

Leave a Reply

%d bloggers like this: