Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya koma kan kujerarsa ta shugabantar kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar APC

0 86

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya koma kan kujerarsa ta shugabantar kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar APC, bayan dawowarsa daga kasar waje domin neman magani.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar a yau a Damaturu ta hannun Mamman Mohammed, darakta janar na harkokin yada labaran gwamnan.

Mamman Mohammed yace Mai Mala Buni ya roki dukkan ‘ya’yan jam’iyyar da su kwantar da hankulansu tare da zama masu bin doka da oda.

Mai Mala yace bata lokaci ne ya rike mutum a zuciyarsa, cikin wadanda ke da hannu a abubuwan da suka faru a jam’iyyar a ‘yan kwanakinan, inda yace hakan ma zai iya kawo matsala ga nasarar jam’iyyar.

Gwamnan ya bayyana godiya ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa yadda ya shawo kan rashin fahimtar junan da aka samu a jam’iyyar ‘yan kwanakinnan.

Buni yace dukkan matakan da kwamitin ya dauka karkashin shugabancin gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja, wanda yayi rikon kwarya, suna nan bisa doka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: