Ofishin kula da basusuka na kasa yace bashin da ake bin Najeriya zuwa watan Disambar bara ya kai naira tiriliyan 39 da miliyan dubu 550

0 44

Ofishin kula da basusuka na kasa yace bashin da ake bin Najeriya zuwa watan Disambar bara ya kai naira tiriliyan 39 da miliyan dubu 550.

Darakta Janar ta ofishin kula da basussukan, Patience Oniha, ta fadi haka a yau lokacin da take jawabi ga manema labarai dangane da halin da ake ciki akan basukan da ake bin kasarnan.

Patience Oniha tace adadin bashin ya kunshi jumillar basukan da ake bin Najeriya a cikin kasa da kasashen waje, da gwamnatocin jihsohi 36, tare da babban birnin tarayya.

Idan za a iya tunawa dai, ofishin kula da basukan tun a baya ya sanar da cewa basukan da ake bin kasarnan zuwa watan Satumbar bara, ya kai naira tiriliyan 38.

Tace karuwar basukan da aka samu sun hada da sabbin basukan da gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihoshi suka ciyo.

A cewar Patience Oniha, har yanzu basukan da ake bin kasarnan basu wuce hankali ba.

Sai dai, tace gwamnatin tarayya ta dauki manyan matakai wajen magance kalubalen tara kudaden shiga wadanda ke jawo wahalhalu wajen rage yawan basukan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: