Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar wata guguwa mai suna Gombe a kasar Mozambique sun kai 48, kuma hanya daya tilo da ta isa yankin da lamarin ya fi kamari ta lalace.

Guguwar Gombe ta shafi dubun dubatar mutane tun bayan da ta sauka a makon jiya.

Rahotanni sun ce akalla gidaje dubu uku ne suka lalace.

A cewar hukumomi, yankin Mossuril da ke lardin Nampula a arewacin kasar shi ne yankin da lamarin ya fi shafa inda mutane 31 suka mutu.

Har yanzu ba a iya zuwa yankin, sanadiyyar lalacewar hanyoyin mota da na wayar tarho.

Cibiyoyin kiwon lafiya da makarantu da gonakin noma na yankin sun lalace.

Hukumar bayar da agaji ta kasar ta ce za ta taimakawa iyalan da abin ya shafa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: