Jam’iyyar PDP ta kayyade kudi naira miliyan 40 a matsayin kudin fom na takarar shugaban kasa

0 68

Jam’iyyar PDP ta kayyade kudi naira miliyan 40 a matsayin kudin fom na takarar shugaban kasa.

Jam’iyyar ta amince da hakan ne a taron kwamitin zartarwa na kasa na jam’iyyar da aka gudanar jiya a Abuja.

Jam’iyyar ta kuma amince da fara sayar da fom daga yau.

Bisa ka’idojin da aka fitar jiya, ‘yan jam’iyyar PDP masu neman kujerar gwamna za su biya jumillar naira miliyan 21.

Masu neman takarar sanata za su biya jimillar naira miliyan 3 da rabi, sannan kuma masu neman takarar majalisar wakilai za su biya naira miliyan 2 da rabi.

Masu neman takarar majalisar dokokin jihoshi za su biya naira dubu 600.

Kazalika jam’iyyar ta amince da rage kashi 50 cikin 100 na kudaden takara ga matasa masu shekaru 25 zuwa 30 na mukamai daban-daban.

Leave a Reply

%d bloggers like this: