Gasar Kofin Duniya: An Bar Messi A Benci A Wasan Ƙarshe Na Rukunin Argentina
Tauraron ƙwallon ƙafa na Argentina, Lionel Messi, zai fara daga benci lokacin da ƙasarsa za ta kara da Jordan a wasanta na ƙarshe a matakin rukuni na Gasar Kofin Duniya.
Argentina ta riga ta tabbatar da tsallakewa zuwa zagayen gaba a matsayin ta ɗaya a rukuninta bayan nasarar da ta samu a kan Algeria da Austria.
Messi ya taka rawar gani a gasar, inda ya ci hat-trick a wasan farko sannan ya ƙara kwallaye biyu a karawa da Austria. Jimillar ƙwallayensa biyar ta sa ya zama wanda ya fi kowa cin ƙwallaye a tarihin Gasar Kofin Duniya da ƙwallaye 18, sannan shi ne ke jagorantar masu cin ƙwallaye a gasar ta bana.
Kocin Argentina, Lionel Scaloni, ya tabbatar a taron manema labarai kafin wasan cewa ba zai saka Messi cikin ‘yan wasan da za su fara wasan ba domin ba shi hutu.
Scaloni ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayar fitaccen ɗan jaridar Argentina, Macaya Márquez, mai shekaru 93, wanda ke ruwaito Gasar Kofin Duniya karo na 18.
Kocin ya ce, “Messi ba zai fara wasan ba,” yana mai yabawa tsohon ɗan jaridar saboda irin gudunmawar da ya bayar a aikin jarida.
Ana sa ran Argentina za ta yi sauye-sauye a cikin jerin ‘yan wasanta domin mayar da hankali kan wasannin zagayen gaba, bayan ta tabbatar da matsayinta a saman rukunin.
Sai dai ana sa ran Messi zai dawo cikin jerin ‘yan wasan farko a wasan zagaye na 32 da Argentina za ta buga da Cape Verde a ranar 3 ga Yuli, yayin da take neman kare kambun Gasar Kofin Duniya.