Gaskiyar Kuɗin Kwangilar Layin Dogon Lagas – Ibadan

0 148

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce kudin ayyukan layin dogo daga Legas zuwa Ibadan dala bilyan 1.58 ne, ba dala bilyan biyu ba, kamar yadda wasu kafafen yada labarai ke yadawa.

Sakataren ma’aikatar sifuri ta kasa Sabi’u Zakari ya bayyana hakan cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan watsa labarai na ma’aikatar Anastasia Ogbonna ya rabawa manema labarai a Abuja.

Ya ce aikin zai bukaci dala milyan 4.9, ba kamar yadda wasu kafafen yada labarai ke batun cewa za a kashe dala milyan 13 ba.Sakataren ya bada tabbacin cewa hanyar layin dogon ta Legas zuwa Ibadan tuni an fara gudanar da kuma yana daga cikin ayyukan da wannan Gwamnatin ta sa gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: