Gidauniyar Masarautar Gumel ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Jigawa da ta faɗaɗa tare da inganta hanyar Maigatari-Gumel zuwa hanya mai hannu biyu, la’akari da ƙaruwar zirga-zirgar ababen hawa da kuma bunƙasar harkokin kasuwanci a yankin.
Shugaban Kwamitin Amintattu na Gidauniyar, Alhaji Mohammed Sani Ahmed, wanda kuma shi ne Dan Amar na Gumel, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Gumel.
Ya ce hanyar na da muhimmanci ga tattalin arzikin yankin, musamman duba da yadda harkokin kasuwanci da zirga-zirgar jama’a ke ƙara ƙaruwa a tsakanin ƙananan hukumomin da ke kan hanyar da kuma maƙwabtan ƙasashe.
Alhaji Mohammed Sani Ahmed ya bayyana cewa faɗaɗa hanyar zuwa mai hannu biyu zai taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa, inganta zirga-zirga da kuma rage haɗurran mota, tare da ƙara bunƙasa kasuwanci da hulɗar tattalin arziki a yankin.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta ba da fifiko ga aikin, yana mai cewa hakan zai kawo ci gaba mai ɗorewa ga al’ummar yankin Gumel da Maigatari.
