Gobara ta ƙone motoci da rumfunan katako takwas da kuma kayan aikin kafinta ƙurmus

0 169

Wata gobara ta ƙone motoci takwas ƙurmus da rumfunan katako takwas da kuma kayan aikin kafinta a layin Lawan Dambazau daura da digar jirgin kasa da ke Unguwar Gandu a Jihar Kano.

Lamarin ya faru a jiya Talata ya auku ne a wani kango da ake aikin kafinta da gyaran mota.

A cewar jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif Abudullahi, jami’an hukumar sun isa wurin ne bayan samun kiran gaggawa daga Ofishin ’yan sanda na Kwalli.

Ya ƙara da cewa an yi amfani da motocin kashe gobara 5 da suka kawo ɗauki reshensu na Sakatariyar Audu Bako da ofishin kwana-kwana da ke Sharaɗa.

BAS

Leave a Reply

%d bloggers like this: