‘Yan bindiga sun kashe babban limamin masallacin Juma’a na kauyen Keita

0 154

Wasu ‘yan bindiga sun kashe Sheikh Ahmad Rufa’i, babban limamin masallacin Juma’a na kauyen Keita a karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Kisan Sheikh Rufa’i ya zo ne bayan makonni uku da kashe Imam Abubakar Hassan Mada, limamin babban masallacin Mada a karamar hukumar Gusau ta jihar.

Wani mazaunin Keita, Ibrahim Musa Keita, ya ce ‘yan bindigar sun mamaye kauyen ne jim kadan bayan da musulmi suke yi sallar isha’i. Ya yi bayanin cewa, “Kafin mamayar, an sanar da mazauna garin game da motsin ‘yan bindigar a kan titin Kwarin Gano-Keita.

Leave a Reply

%d bloggers like this: