Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sanya takunkumi ga wasu manyan makarantun Najeriya

0 161

Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sanya takunkumi ga manyan makarantun da suka sabawa ka’idar tsarin raba daidai na tarayya wajen daukar ma’aikata, inda ta kafe cewa hakan abu ne da ya zama tilas.

Daraktan hulda da jama’a da sadarwa na hukumar da’ar ma’aikata ta tarayya Dokta Chuks Okoli, shi ne ya bayyana haka a Abuja.

Ya ce hukumar ta lura da yadda a yanzu wasu manyan makarantun tarayya suka fara aikin daukar ma’aikata ba tare da bin umarnin hukumar ba, wajen tabbatar da daidaito, da adalci bisa amfani da sashe na 14 (B) na kundin tsarin mulkin tarayya. Ya yi nuni da cewa takardar da aka fitar daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, ta ce ko kadan makarantun tarayya ba su bi tsarin raba daidai ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: