Nan ba da dadewa ba majalisar dattawa za ta dage dakatarwar da ta yi wa Sanata Abdul Ningi

0 91

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce nan ba da dadewa ba majalisar za ta dage dakatarwar da ta yi wa Sanata Abdul Ningi na jam’iyyar PDP, mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya.

Hakan na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da dan majalisar ya rubuta wa Akpabio takarda, inda ya yi barazanar daukar matakin shari’a idan ba a dage dakatarwar da aka yi masa ba cikin kwanaki 7.

An dakatar da Ningi ne biyo bayan wata hirar da ya yi da BBC Hausa inda ya yi zargin cushe a kasafin kudin bana.

Bayan zazzafar muhawara da yan majalisar suka yi a zauren majalisa kan lamarin, an dakatar da Ningi na tsawon watanni uku tare da neman ya rubuta wasikar neman gafara ga majalisar. Sai dai a wata takarda da lauyan sa Femi Falana (SAN) ya rubuta, Ningi ya zargi Akpabio da kasancewa mai tuhuma, mai gabatar da kara da kuma alkali kan lamarin, inda ya ce hakan ya sabawa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Leave a Reply

%d bloggers like this: