Kwamitin Masallacin Dutse ya raba buhunan Shinkafa buhu 30,000 ga zawarawa da sauran marasa galihu

0 121

Babban Kwamitin Masallacin Dutse da ke jihar nan ya raba buhunan Shinkafa buhu 30,000 mai nauyin kilogiram 10 ga zawarawa da sauran marasa galihu a fadin kananan hukumomin jihar 27.

Babban limamin masallacin Dr Abubakar Birninkudu yayin da yake kaddamar da rabon tallafin da aka gudanar a babban masallacin Dutse, ya ce shinkafar wani bangare ne na taimakon da gidauniyar Aliko Dangote ta tura jihar Jigawa.

Dokta Birninkudu ya bayyana cewa, Gidauniyar Aliko Dangote ce ke bayar da shinkafar ga al’ummar jihar JIgawa domin a samu saukin rayuwa a wannan wata na Ramadan. Da yake jawabi a wajen kaddamarwar, hakimin Dutse, Alhaji Jamilu Basiru Sunusi ya yabawa gidauniyar bisa wannan karimcin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: