Wata gobara da ba a san musabbabinta ba ta kone gidan Malam Shafi’u Rafa, inda ta jawo mutuwar yayansa biyu, yayin da ta lalata kayan abinci da dabbobi da dubban nairori.

Lamarin, a cewar jami’an yada labaran karamar hukumar Buji, Ali Safiyanu, ya auku a kauyen Rafa mai nisan kilomita kalilan da ga helkwatar karamar hukumar Buji ta jihar Jigawa.

Sai dai, ba a gano musabbabin tashin gobarar ba, amma ta kashe Fatima Shafi’u mai shekaru 4 a duniya da Firdausi Shafi’u, yar shekara 7.

Gobarar ta kuma lalata dakuna shida, da dabbobin gida da kayan abinci.

Da aka nemi jin ta bakinsa, daraktan hukumar kashe gobara, Malam Haruna, yace bashi da masaniya kan lamarin, inda yace har yanzu yana jiran kwamandan yan kwana-kwana na shiyyar Birnin Kudu ya sanar da shi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: