Gobara ta yi wa mutane kimanin 120 sanadiyyar rasa matsugunni

0 212

Wata gobara da ta afku a rukunin gidaje na Megida Onikanhun da ke Edun Isale a karamar hukumar Ilorin ta Kudu, ta yi sanadiyyar rasa matsuguni ga mutane kimanin 120 tare da kone dakuna 44 na wani gini da wani masallaci.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Hassan Adekunle da aka fitar a jiya Litinin a Ilorin.

Sanarwar ta ce a ranar 15 ga watan Janairu da misalin karfe 11:08 hukumar kashe gobara ta jihar Kwara ta karbi wani rahoto kan gobarar da ta tashi a harabar Megida Onikanhun da ke Edun Isale a karamar hukumar Ilorin ta Kudu.

Adekunle ya yaba da kokarin hukumar kashe gobara amma ya ce lamarin ya bar mutane sama da 120 ba matsuguni, lamarin da ya shafi dakuna 44 da masallaci, amma ba a samu asarar rai ba a a ginin mai dakuna 75. Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Mista Falade Olumuyiwa, ya bukaci jama’a da su rika yin taka tsan-tsan wajen kare duk abinda zai janyo tashin gobara, musamman a wannan lokaci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: