INEC ta ce a shirye take tsaf domin gudanar da zaben cike gurbi a jihar Cross River

0 174

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa, INEC, ta ce ta shirya tsaf domin gudanar da zaben cike gurbi da zai gudan a ranar 3 ga watan Fabrairu a jihar Cross River.

Shugabar wayar da kan jama’a da masu kada kuri’a ta INEC a jihar, Anthonia Nwobi, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a yau Talata a Calabar.

Nwobi ta ce za a sake gudanar da zaben ne a mazabu 34 da ke fadin mazabar tarayya ta Akamkpa da Biase, Obanliku da Yala tabiyu, a Jiha.

Ta ce masu katin zabe na dindindin ne kadai aka yarda su kada kuri’a, a yankunan da abin ya shafa a lokacin zaben. Ta kuma yi kira ga masu kada kuri’a a yankunan da abin ya shafa da su fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri’a su zabi ‘yan takarar da suke so.

Leave a Reply

%d bloggers like this: