Tinubu ya gana da hafsoshin tsaro a fadar gwamnati dake Abuja

0 107

Shugaba Bola Tinubu ya gana da hafsoshin tsaro da sauran manyan jami’an tsaro a fadar gwamnati da ke Abuja ranar Talata.

Shuwagabannin tsaron sun iso fadar tare da jiran shugaban kasa ya iso daga wani aiki a wajen fadar gwamnati.

Hafsan hafsoshin su ne babban hafsan tsaro na kasa, Janar Christopher Musa; Babban Hafsan Soji, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja; Babban Hafsan Sojan Sama, Air Marshal Hassan Abubakar, da Shugaban Rundunar Sojojin Ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla.

Taron wanda kuma ya samu halartar mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ana sa ran zai tattauna matsalolin ta’addanci, garkuwa da mutane da kashe-kashe a fadin kasar nan.

A halin da ake ciki, Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya kira wani muhimmin taro tare da tawagar rundunonin yan sanda, a ranar 15 ga watan Janairu, domin magance matsalar rashin tsaro a kasar nan. Kayode Egbetokun, din ya nuna matukar damuwarsa kan yadda ake yin garkuwa da mutane a babban birnin tarayya Abuja, inda ya kuma jaddada bukatar daukar kwararan matakai domin dakile irin wadannan munanan laifuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: