Guguwa ta lalata sama da gidaje a 450 a garin Kuletu da ke jihar Bauchi

0 138

Wata guguwa ta abkawa al’ummar Kuletu da ke karamar hukumar Dass a jihar Bauchi, lamarin da ya shafi gidaje sama da 450.

 lamarin ya faru ne da yammacin Lahadi 15 ga watan Yuni, da misalin karfe 4:47 na yamma, inda wata iska ta afkawa yankin, ta yayyaga rufin  dakuna tare da raba dukiyoyi da kuma lalata wasu gine-gine gaba daya

Wani mazaunin garin da ke jagorantar duba barnar da al’umma suka yi, mai suna Jibrin Abdullahi, ya ce kawo yanzu gidaje 452 ne aka kidaya a matsayin wani bangare ko kuma sun lalace gaba daya.

A cewarsa, “suna cikin wani yanayi na ban tausayi, wasu gidaje sun ruguje gaba daya, yayin da wasu kuma suka rasa rufin dakunansu, yawancin jama’ar yankin yanzu ba su da matsuguni, kuma suna bukatar agajin gaggawa.

Leave a Reply