Bai kamata a yi shiru kan kashe-kashen Benue ba – Atiku

0 144

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da sauran shugabannin siyasa da su dauki matakin gaggawa don magance tashe-tashen hankula da zubar da jini a Jihar Binuwe, inda ya bayyana cewa kashe-kashen ya kai ga wani matakin da ba za a iya jurewa ba.

A wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin a shafinsa X, Atiku ya yi Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin ci gaba da yin shiru da halin ko in kula da hukumomi ke yi dangane da “gaskiya mai ratsa zuciya” a Benuwe da sauran sassan kasar nan da hare-haren ta’addanci ya shafa. Zubar da jinin da aka yi a jihar Benue ya kai wani mummunan yanayi – gaskiya ce mai ratsa jiki da ratsa zuciya wadda ba za a iya yin watsi da ita ba,” in ji Atiku”.

Leave a Reply