‘Gwamna Badaru Abubakar kokarin raba kan yan jam’iyyar APC ta jihar Jigawa yake’ a cewar wasu jiga-jigan jam’iyyar

0 125

Wasu daga cikin jiga-jigan APC kuma mambobin kungiyyar dattawan jihar Jigawa, sun aikewa shugaban rikon kwarya na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, takardar koken a soke zaben shugabannin jma’iyyar na jihar da aka gudanar, inda suka ce gwamna Muhammadu Badaru Abubakar yana kokarin raba kan yan jam’iyyar ne.

Mambobin sun bukaci kwamitin ya gaggauta rusa zaben da aka gudanar a kwanakin baya.

Kafin hakan dai dattawan a ranar 30 ga watan Oktoba na 2021 sun taba rubuta wata takardar korafi, sannan a ranar 23 ga watan Disamba ma na 2021 suka sake tinawa kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar.

Wannan takardar koken na dauke da sa hannun jiga-jigan jam’iyyar 6, wadanda suka hada da Alhaji Sani Ibrahim Taura, Barrister Hafizu Abubakar, Alhaji Bala Idi Kazaure, Mutari Garba Garki da kuma Saifullahi Muhammad Mudasshir.

Suna zargin gwamnan da cewa yayi gaban kansa wajan gudanar da zaben shuwagabannin jam’iyyar, tare da cimma jarjeniyar cewa Alhaji Aminu Sani Gumel ya zama shugaban jam’iyyar na jiha tare da wasu shugabannin jam’iyyar 35.

Leave a Reply

%d bloggers like this: