Dalilan da yasa na dage dokar kullen hawa babura a jihar Yobe – Maimala Buni

0 36

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya dage dokar hana babura masu kafa biyu a kananan Hukumomi 10 dake arewa da kudancin jihar.

Buni ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a fadar mai martaba Sarkin Nguru, a lokacin dayakai ziyarar jajantawa mutanen da sukayi asara a gobarar data tashi ranar asabar a babbar kasuwar Nguru dake jihar.

Inda yace yanzu gwamnati ta amince mutane su fara hawa babura domin zuwa gonakin su da kuma wasu ayyukansu na yau da kullum.

Ya kara da cewa sundauki wannan matakin ne biyo bayan samun cigaban da akayi a fannin tsaro a yanki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: