A karo na biyu cikin mako guda Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami a kan iyakarta da Koriya ta Kudu.

Ta kuma gwada  makamin nata ne a wayewar garin yau da misalin karfe 7 da mintina 27 na safe.

Firaministan Koriya ta Kudu Fumio Kishida bai ɓata lokaci ba wurin sukar halayyar makwabciyar tasa.

Gwajin na zuwa a lokacin da kwamatin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ke zama don tattauna yadda za a ɓullo wa take-taken Koriya ta Arewa, wadda ba ta daddara da takunkuman da aka kakaba mata ba kawo yanzu.

Wakilin BBC ya ce gwamnatin Pyonyang na gwajin makaman ne don janyo hankalin Amurka ta dawo teburin tattaunawa da Shugaba Kim Jong Un.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: