Gwamna Badaru ya ce mutumin kirki wanda ya iya mu’amala shi zai gajeshi a shekarar 2023

0 114

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, ya ce mutumin kirkiri wanda ya Iya Mu’amala da Mutane ne zai gajeshi a Kujerar Gwamnan Jihar Jigawa a shekarar 2023.

A shekarar 2015 da kuma 2019 ne aka zabi Gwamna Badaru Abubakar, a matsayin Gwamnan Jihar Jigawa karkashin tutar Jam’iyar APC.

Gwamna Badaru Abubakar, ya ce dole wanda zai gajeshi a shekarar 2023 ya zama mutumin da yake saurarar koken Jama’a, yadda ya kamata.

Gwamna Badaru ya saba da Takwaransa na Jihar Akwa Ibom Udom Emmanuel, inda ya dauko Kwamishinan Kasa da Albarkatun Ruwa Pastor Umo Eno, a matsayin wanda zai gajeshi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: