Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, ya kai ziyarar neman shawari ga shugabannin PDP reshen jihar Zamfara, yayin da yake shirin takarar Shugaban Kasa a 2023.

Manema Labarai sun rawaito cewa GwamnaTambuwal ya fara neman shawari daga masu ruwa da tsaki na PDP dake jihohi 36 a Najeriya a wani yunkurin neman tikitin takarar shugaban ƙasa.

Gwamnan ya samu kyayyawar tarba daga mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mahdi Aliyu Gasau, da sauran masu faɗa a ji na jam’iyyar PDP.

Da yake jawabi, Tambuwal yace ya zo Zamfara ne domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki a wani ɓangare na cimma burinsa na samun tikitin takarar PDP a zaɓen 2023.

Gwamnan ya ƙara da cewa duk da yasan shirin da ake na tsige mataimakin gwamna, amma ba zai ce komai ba game da lamarin saboda yana gaban Shari’a.

Tambuwal ya gode wa shugabannin PDP bisa kyakkyawar tarban da suka masa duk da halin rashin tsaro da Zamfara ke ciki, inda ya jaddada cewa PDP ce zata kwace jihar a 2023.

A na shi jawabin, Mataimakin Gwamnan Zamfara, Mahdi Gusau, ya ce yana goyon bayan kudirin takarar shugaban ƙasa na gwmana Tambuwal.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: