Gwamna Badaru ya ce zaman lafiya da samar da wutar lantarki a jihar Jigawa ya jawo hankalin kamfanonin sarrafa shinkafa

0 118

Gwamna Mohammed Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya ce zaman lafiya da samar da wutar lantarki a jihar ya jawo hankalin kamfanonin sarrafa shinkafa a fadin jihar.

Badaru, wanda ya bayyana haka a jiya a wajen wani taro da kwamitin kula da harkokin kasuwanci na fadar shugaban kasa ta shirya a Dutse, ya bayyana cewa jihar ta samu ci gaba matuka a fannin samar da wutar lantarki.

Gwamnan ya ce tuni gwamnatin jihar ta tsara wasu manyan tashoshin wutar lantarki guda 4 da za a kafa a kananan hukumomin Kazaure, Babura, Birninkudu da Gwaram.

Ya kuma jaddada cewa, akwai wasu tashoshin samar da wutar lantarki a jihar nan ba da jimawa ba, wanda za a yi a karkashin kungiyar gwamnonin Arewa, karkashin jagorancin gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai.

Badaru ya ce, a yau a jihar Jigawa akwai masana’antu da dama da ke tasowa a kewayen Gagarawa/Gumel saboda wutar lantarkin da ake samu na tsawon sa’o’i 24 a yankin daga tashar wutar lantarki ta Gagarawa.

Shima da yake jawabi a wajen taron, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin kasuwanci a saukake, Dr Jumoke Ojuwale ta ce akwai hadin gwiwa a zahiri tsakanin gwamnatin tarayya da jihar kan shirin saukaka harkokin kasuwanci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: