Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana yadda gwamnatinsa ta ceci tsarin fansho na hadin gwiwa tsakanin jiha da kananan hukumomi daga rugujewa, inda ya ce gwamnatin sa ta shigo da sabbin gyare-gyare domin inganta walwalar ma’aikata da masu ritaya a jihar.
A yayin bikin ranar ma’aikata da aka gudanar a Mallam Aminu Kano Triangle da ke Dutse, Gwamna Namadi ya ce an zuba sama da naira biliyan bakwai domin farfado da tsarin fanshon, tare da soma duba dokar tsarin don cire kurakurai da tabbatar da dorewarsa.
A cewar shugaban ma’aikatan jihar, Muhammad Dagaceri, an sallami kamfanonin kula da kudin fansho guda biyar saboda gazawarsu, inda aka maye gurbinsu da sabbin masu kula da dukiyoyin hukumar. Binciken jaridar PREMIUM TIMES ya nuna cewa kananan hukumomi 27 sun kasa biyan kudadensu na fansho wanda ya kai sama da naira biliyan uku daga shekarar 2014 zuwa 2021, lamarin da ya kara durkusar da tsarin kafin wannan ceto daga gwamnatin yanzu ta yi.