Gwamna Bassey Otu ya ce kyakkyawan shugabancin Bola Ahmed Tinubu ne ya fara jawo hankalin gwamnoni da manyan ƴan siyasa zuwa APC Wannan kalamai na gwamnan Kuros Riba na zuwa ne bayan Gwamnan Delta da manyan jiga-jigan PDP sun sauya sheƙa zuwa APC a makon jiya.
Gwamna Otu ya ce a baya Kuros Riba ce kaɗai jihar da APC ke mulki a Kudu maso Kudu amma yanzu Edo da Delta sun haɗe da ita don kawo ci gaba.
Gwamnan jihar Kuros Riba, Bassey Otu, ya ce tururuwar da manyan ƴan siyasa ke yi zuwa APC na da nasaba da ayyukan alherin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke yi. Gwamna Otu ya bayyana cewa ko kaɗan yawan shiga jam’iyyar APC da ake yi ba shi da nasaba da lissafin siyasa, illa kawai mutane sun gamsu da nasarorin Shugaba Tinubu.
Otu ya fadi haka ne yayin taron karbar Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, wanda ya koma APC a hukumance, kamar yadda Leadership ta ruwaito.