Gwamna Zulum ya kaddamar da mafarauta ‘yan sa kai su 1000 domin yaki da ta’addanci

0 76

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya kaddamar da mafarauta ‘yan sa kai su dubu 1, domin agazawa kokarin da hukumomin tsaro ke yi  na yaki da ta’addanci.

Da yake yiwa mafarautan jawabi a kauyen Khaddamari dake yankin karamar hukumar Jere ta jihar Borno, Gwamna Zulum ya yaba musu bisa sadaukar da kai da goyon bayan da suke bai wa gwamnatinsa a kokarinta na dabbakar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

Gwamnan ya tabbatar musu da tallafinsa na kayan aiki da alawus-alawus na wata-wata domin karfafa musu gwiwa a aikin da suka sanya a gaba.

Ya kuma yabawa wani dan majalisar tarayya, Ahmed Satomi, dake wakiltar Jere a jihar Borno, da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar ta Borno na kananan hukumomin da lamarin ya shafa, bisa gudunmawar da suka bayar wajen hada kan mafarautan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: