Tanko Al-Makura, ya mayar da martani dangane da rahoton cewa EFCC ta kama shi

0 76

Tsohon Gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura, ya mayar da martani dangane da rahoton cewa hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kama shi a ranar Laraba.

Wata sanarwa a jiya da babban sakataren yada labaransa, Danjuma Joseph, ya fitar, tsohon gwamnan yace ba kama shi aka yi ba, gayyatarsa aka yi.

An rawaito yadda hukumar ta EFCC ta tafi da Al-Makura tare da matarsa inda ta tsare su, bisa zarge-zargen rashawa.

Al-Makura ya rike mukamin Gwamnan jihar Nasarawa tsakanin shekarar 2011 zuwa 2019, kafin a zabe shi a matsayin sanata mai wakiltar jihar Nasarawa ta Kudu.

Hukumar EFCC ta sanar da cikakken bayanin zarge-zargen da ya jawo kama sanatan da matarsa ba, wadanda aka bayar da rahoton cewa suna amsa tambayoyi har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Sai dai, da aka tuntube shi, hadimin na Al-Makura yace bashi da masaniyar kama ubangidan nasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: