“Indai mun hada kanmu nayi imanin babu makawa Jamiyyar PDP ce za ta karbi mulkin Najeriya a zabe mai zuwa”, Sule Lamido

0 103

Kamar yadda RFI ta wallafa tace, “Tsohon gwamnan jihar Jigawa a Najeriya kuma Kusa a jamiyyar PDP mai adawa Alhaji Sule Lamido, ya ce ba wani abin mamaki a game da yadda shugaban kasar Muhammadu Buhari ke tafiyar da mulkar kasar, saboda a cewarsa shugaban na kallon kasar da kuma abin da ke ciki a matsayin ganimar nasarar da ya yi a zabe.

To sai dai tsohon gwamna Lamido, ya ce ya yi imanin babu makawa Jamiyyarsu ta PDP ce za ta karbi mulkin Najeriya a zabe mai zuwa, amma da sharadin ‘yayan jam’iyyar za su hada kansu”.

Leave a Reply

%d bloggers like this: