Kamfanin Samar da Kayan Noma na Jihar Jigawa (JASCO) zai sayar da tirela 200 ta taki ga manoman damina

0 97

Kamfanin Samar da Kayan Noma na Jihar Jigawa (JASCO) zai sayar da tirela akalla 200 ta takin zamani ga manoman damina a fadin kananan hukumomin 27 na jiharnan.

Manajan daraktan kamfanin, Rabi’u Khalid Maigatari wanda ya tabbatar da samar da takin zamani samfurin NPK da Urea ya ce tuni jihar ta fara siyarwa kai tsaye daga ranar Litinin kamar yadda gwamnan jiha Muhammad Badaru Abubakar ya umarta.

Rabi’u Khalid ya bayyana cewa tuni kamfanin ya raba sama da tirela 100 na takin NPK ga manoman rani yayin da wasu da dama suka samu Urea a guraren sayarwa akalla 30 a fadin jiharnan.

Ya ce kamfanin yana sayar da takin NPK a kan naira dubu 8 da 500 yayin da yake sayar da Urea akan naira dubu 11 da 500, inda ya kara da cewa tashin farashin ya samo asali ne daga karin kayayyakin da ake amfani da su wajen sarrafa takin da hada shi.

Ya kuma ce kamfanin yana da alhakin samar da ingantattun iri na amfanin gona iri-iri kamar su dawa da gero da wake da shinkafa da alkama da ridi da sauransu, wadanda suma ana samunsu a wadannan guraren sayarwar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: