Karamar hukumar Hadejia ta raba magunguna da kudin su yakai kimanin Naira dubu 100 ga cibiyar lafiya

0 66

Karamar hukumar Hadejia ta raba magunguna da kudin su ya tasamma  Naira dubu 100 ga cibiyar lafiya matakin farka a karamar hukumar Hadejian.

A jawabinsa yayin mika maganin ga Shugaban cigiyar magunguna na karamar hukumar Hadejia Alh Abdulkadir Bala Umar yace za araba magungunan ne ga cibiyoyin lafiya, ya ce hakan na a matsayin wani yunkuri da suke domin tallafawa masu fama da cutar amai da gudawa.

Shugaban karamar hukumar ya umarci cibiyoyin lafiya matakin farko da suyi amfani dasu ta hanyar da ta dace, daga nan ya jinjinawa gomnatin jihar Jigawa bisa kokarin da take a fannin lafiya.

Alh Abdulkadir Bala Umar ya yi kira alumar karamar hukumar Hadejia da a cigaba da tsaftar muhalli, da kuma yashe magudanan ruwa domin kare kai da cutuka.

Kazalika ya bukaci aluma da suyi gaggawar daukar marasa lafiya da akayi zargin ya fara nuna alamonin cutar mai saurin galabaitarwa zuwa cibiyar lifuya mafi kusa. Alhaji Idris Wada wanda shine Shugaban hukumar lafiya matakin farko a karamar hukumar Hadejia yayin jawabinsa ya jinjinawa karamar hakuma da wannan kokari tare da alkawarin cewa zusu yi amfani da wannan dama domin ganin an yaki cutuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: