Gwamnan Babban Bankin Kasa (CBN), Godwin Emefiele, ya bukaci gwamnoni jihoshi 36 da su kara zuba jari a bangaren gona domin habaka tattalin arzikin jihoshinsu.
Emefiele wanda yayi jawabi a Fatakwal a jiya a wajen kaddamar da kamfanin sarrafa rogo na jihar Rivers, yace gwamnoni su zuba jari a amfanin gonar da suke da shi.
Gwamnan na CBN yace kamfanin zai taimaka wajen inganta samarwa da sarrafa rogo zuwa garin fulawa mai inganci a jihar Rivers.
Emefiele yayi nuni da cewa samar da gonaki ne babbar matsalar da ake fuskantar wajen ayyukan noma a yankunan kudancin kasarnan saboda yanayin kasar can.
Ya kuma ce jihoshin yankin kudu maso kudu sun ci gajiyar kimanin naira biliyan 7 da miliyan 436 domin samar da karin gonakin noma, da samar da hanyoyin zuwa gonaki, da samar da kayan aikin gona, da sauran abubuwan tallafi a yankin.