Gwamnan jihar Ebonyia ce yana addu’ar Allah ya sake ba wa ƴan Najeriya mai kyakkyawar zuciya kamar Shugaba Buhari

0 241

Gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ya ce yana addu’ar Allah ya sake ba wa ƴan Najeriya shugaba mai kyakkyawar zuciya da kishin kasa kamar shugaba Muhammadu Buhari a zaɓen 2023.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da Manema Labarai na fadar shugaban Kasa, bayan ganawa da shugaba Buhari a Abuja.

Haka kuma gwamnan na jinjina wa shugaban ƙasar kan wasu manyan ayyukan ci gaba da gwamnatinsa ta samar a yankin kudu maso gabashin Najeriya tun bayan hawansa mulki a 2015.

Gwamnan ya bayyana ayyukan jirgin Kasa zuwa yankin kudu maso kudu wanda ya ce zai sake bunkasa kasuwancin yankin.

David Umahi ya ce ya gana da shugaba Buhari ne domin ya mika masa godiya ta musamman saboda yadda yake daukar yankin kudu maso kudu da muhimmanci.

Kazalika, ya ce yayi kusa a fara zancen mikawa yankin kudu maso kudu takarar shugabancin kasa a shekarar 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: