Shugaba Buhari yayi kira ga yan inshora da su billo da sabbin dabarun wajen samar da kudaden shiga ga kasarnan

0 82

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi Kira ga hukumomin inshora a Najeriya su billo da sabbin dabarun zamani wajen samar da kudaden shiga ga kasarnan, a yunkurin da gwamnati keyi na rage dogaro da Man fetur kacokam a Matsayin hanyar samun kudin shiga.

Shugaban ya kuma yabawa hukumar kan gudumawar da take bayarwa na karfafa gwiwar likitocin kasar a yakin da suke da Cutar Corona a Najeriya 

Buhari yayi wannan jawabi ne ta Bidiyon kai tsaye yayin babban taron bikin kungiyar Inshora ta Nahiyar Afirka na shekara shekara karo na 47

Shugaba Buhari yace fannin inshorar zai taimaka matuka gaya, wajen fadadawa dama bukasa tattalin arziki kasar nan,

Tare da samar da kyakyawan yanayin da zaisa a samu karin kudaden haraji, da samar da aikinyi a kuma fadada hanyoyin samun kudaden shiga a kasar.

Shugaban ya kuma yiwa taron na bana take da “sake farfado da tattalin Arzikin Nahiyar Afirka bayan annobar Corona.

Leave a Reply

%d bloggers like this: