Gwamnatin jihar Zamfara tayi luguden wuta kan fitattun sansanonin ‘yan fashin daji a jihar

0 123

Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi ikirarin cewa jiragen yakin rundunar sojin sama sun yi luguden wuta kan fitattun sansanonin ‘yan fashin daji a jihar da ma kewayenta.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da tabada sanarwar rufe abin da ta kira haramtattun tasoshin mota da wasu kasuwanni nan take a fadin jihar.

Wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara Ibrahim Dosara ya fitar ta ce sansanonin da aka tarwatsa a hare-haren sojin saman sun hada da na wani kasurgumin dan fashin daji da ake kira Dan Karami a karamar hukumar Shinkafi.

A cewar sanarwar a baya dan fashin dajin ya fitar da wani bidiyo yana murna bayan artabun da suka yi da sojoji. Mahukuntan jihar Zamfara sun kuma ce sojojin kasa sun yi kwanton bauna kan wasu ‘yan fashin dajin da suka yi kokarin tserewa luguden wutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: