Kwanturola janar ya kama mutum 9 da zasu tsere zuwa kasar Libya a jihar Jigawa

0 187

Kwanturola janar na hukumar shige da fice shiyyar jihar jigawa, Alhaji Ismail Abba Aliyu, ya bayyana wani mutum Alhaji Ibrahim Kano a matsayin wanda hukumar take nema ruwa a jallo.

Da yake jawabi ga manema labarai a Dutse, ya kara da cewa sauran wadanda ake zargi mutane tara an kama su akan hanyar Kazaure, suna wucewa ta kwangolam a kokarin su na isa Birnin Tripoli na Libya ta barauniyar hanya daga hanyar jamhuriyar nijar.

Kwanturola janar din ya kara dacewa, mutane taran da ake zargi sun fito daga jahohi daban-daban, sun kuma hadu a kano domin hawa mota zuwa kasar ta Libya.

Ya kuma kara da cewa, wadanda ake neman mata shida ne da kuma maza uku yan tsakanin shekaru 20 zuwa 30, kuma sun fito ne daga jahohi mabanbanta, daya ya fito daga jihar Eikiti, daya daga jihar Benue, daya kuma daga Oyo, mutane biyu daga Jihar Lagos, sauran mutane hudun sun fiti ne daga jihar Ogun.

Ya kuma ce kwanturola janar na kasa Muhammad Babandede, ya umarce shi da ya damka wadanda ake nema ga hukumar yaki da fataucin mutane ta kasa watau NAPTIP.

Ya kuma shawarci iyayen da sauran al’aumma da su guci tura yayan su kasashen wajen domin samun ingantacciyar rayuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: