Gwamnan Jihar Gombe ya kaddamar da allurar rigakafin shan inna ga Kimanin yara 981,710

0 129

Gwamnan Jihar Gombe Inuwa Yahaya ya kaddamar da allurar rigakafin shan inna ga Kimanin yara 981,710 ’yan kasa da shekara biyar a fadin Jihar Gombe.

Gwamna Inuwa wanda ya samu wakilcin kwamishinan lafiya, Dokta Habu Dahiru, ya ce rigakafin yana daga cikin manufofin shirin

Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakuna na jihar, Mai Kaltungo Injiniya Sale Muhammad, yayi kira ga shugabannin al’umma da iyayen yara musamman mata da su ba da hadin kai wajen ganin an yi wa ’ya’yansu rigakafin kasancewar allurar ba ta da wata illa kuma za ta kare yaran daga cututtuka masu kisa.

Shi ma wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Dokta Ibrahim, ya cei tallafin gwamnatin jihar ke bayarwa wajen magance matsalolin kiwon lafiya ya sa ake ganin nan ba da jimawa ba za a kawar da cutar shan inna da sauran cututtukan yara masu kisa. Dokta Abdurrahaman Shu’aibu Shugaban hukumar kula da lafiya matakin farko a jihar Gombe, ya ce sun kaddamar da allurar rigakafin shan innan ne da tsutsar ciki da cututtukan kananan yara, zazzabin cizon sauro da sauransu, wanda za a dauki tsawon kwanaki hudu daga ranar Asabar 16 zuwa Talata 19 ga watan Disamba 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: