Gwamnan jihar Zamfara ya tattauna da jami’an tsaron Najeriya gameda kawo karshen yan bingida

0 93

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya tattauna da jami’an tsaron kasar nan tare da ziyartar wasu daga cikin wadanda harin yan bingida ya shafa a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin dayake duba sabbin jami’an sojin kasar nan da aka dauka a kananan hukumomin jihar 14.

Matawalle ya kuma nuna takaicinsa bisa kisan kiyashin da akayi wasu mazauna garuruwan Anka da Bukkuyum dake jihar.

Tare da yabawa gwamnatin tarayya bisa ayyana yan fashin daji a matsayin yan ta’adda, a cewar sa hakan zai taimaka wajan kakkabe su baki daya.

Kafin hakan dai cikin bayanan sa, ya bukaci rundunar soji Nigeria, akan tayi amfani da sabbin jiragen yakin nan na Tucano wajan murkushe yan bindiga

Leave a Reply

%d bloggers like this: