Gwamnatin jihar Jigawa ta kashe sama da miliyan 970 wajen samar da ruwan sha

0 75

Hukumar samarda ruwansha da tsaftar muhalli a matsakaitan garuruwa ta jihar Jigawa STOWA tace ta kashe kudi fiye da naira miliyan 977 wajen inganta harkar bada ruwan sha a matsakaitan garuruwa a 2021.

Mukaddashin Manajan Daraktan Hukumar Injiniya Ado Garba Kiyawa ne, ya sanar da hakan ga manema labarai a birnin Dutse jiya Lahadi.

Yace daga cikin adadin kudaden, gwamnati ta kashe kudi naira miliyan 228 wajen gyaran gidajen ruwa masu amfani da hasken rana da man gas guda 160.

Yayinda ta kashe naira miliyan 307 wajen sauya gidajen ruwa masu amfani da man gas zuwa masu amfani da hasken rana guda 22.

Inda kuma ta kashe kudi naira miliyan 404 wajen samarda sabbin gidajen ruwa masu amfani da hasken rana karkashin aiyukan mazabu guda 57 a matsakaitan garuruwa na jihar nan.

Injiniya Garba Kiyawa ya ce a yanzu haka an kammala shirye shiryen gudanar da aiyukan mazabu na kusan naira miliyan dubu 1.

Kawo yanzu hukumar ta sauya gidajen ruwa masu amfani da man gas zuwa masu amfani da hasken rana 172 a matsakaitan garuruwa na jihar Jigawa

Leave a Reply

%d bloggers like this: