Matsalar tsaron da ake fuskantar Najeriya nan bada dadewa ba zata zama tarihi – Irabor

0 114

Babban Hafsan Tsaron kasar nan, Janar Lucky Irabor, ya ce duk da matsalar tsaron da ake fuskantar, nan bada dadewa ba matsalar zata zama tarihi.

Janar Lucky, wanda ya bayyana hakan yayin wani taron ibada na musamman a coci domin tunawa da ranar ’yan mazan jiya, ya ce kalubalen tsaron da kasar ke fuskanta na dab da zama tarihi.

Shi ma a sakonsa na fatan alheri, Babban Hafsan Sojojin Kasa, Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya ce ana shirya taron ne a kowacce shekara domin tunawa da ’yan mazan jiya da suka sadaukar da rayuwarsu wajen hadin kai da cigaban kasa.

Janar Faruk ya ce ba za a taba mantawa da irin gudunmawar da suka bayar ba, sannan ya yi addu’a ga wadanda suka mutu.

Ya kuma ce ci gaba da kula da wadanda suka samu raunuka abu ne da zai ci gaba da zama a kan gaba a rundunar da ke karkashinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: