Shugaba Buhari zai kai ziyara jihar Ogun ranar Alhamis domin kaddamar da wasu manyan ayyuka

0 70

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, zai kai ziyara jihar Ogun A ranar Alhamis, 13 ga watan Janairu, 2022, domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamna Dapo Abiodun ya aiwatar.

Kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ya bayyana cewa, tun farko shugaban ya tsara zuwa Ogun a ranar 21 ga watan Disamba, amma kuma aka ɗage tafiyar sabida wasu dalilai.

Amma yanzun, gwamnatin jihar Ogun, ta bayyana cewa shugaban ya amince da kai ziyarar aiki ta kwana ɗaya ranar 13 ga watan Janairu, 2022.

Sakataren watsa labarai na gwamnan jihar Ogun, Kunle Somorin, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Yace za’a tarbi shugaba Buhari a filin Gateway City Gate Sagamu da misalin karfe 10:00 na safe, inda zai kaddamar da aiki na farko.

Sanarwan ta ƙara da cewa, ana tsammanin shugaban ƙasa, Buhari zai kaddamar da babbar hanyar da ta taso daga Mojoda zuwa Epe.

Haka kuma zai bude sabbin jerin gidaje 2 da gwamnatin jihar ta kammala ginawa a babban birnin jihar, Abeokuta

Leave a Reply

%d bloggers like this: