Hukumar hana ta’ammali da miyagun kwayoyi ta kasa a jihar Jigawa zata bude karin rassanta guda biyu a masarautar Gumel.

Kwamandan hukumar na jiha, Dakta Baraje ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci Mai Martaba Sarkin Gumel, Alhaji Ahmed Muhammad Sani a fadarsa.

Ya ce sashin hana fataucin miyagun kwayoyi akan iyaka ne zai rika lura da kan iyakoki, yayinda sashin sintiri da bincike zai cigaba da sintiri akan tituna.

Daga nan ya bukaci samun goyan baya da hadin kan masarautar domin samun saukin gudanar da ayyukan su.

A nasa jawabin Mai Martaba Sarkin Gumel, Alhaji Ahmad Muhammad Sani ya jaddada bukatar ganin ana lura da tarbiyar Yara a matsayin su na manyan gobe.

Mai Martaba Sarki wanda ya samu wakilcin Galadiman Gumel, Alhaji Usman Muhammad Sani ya ce tuni majalisar masarautar ta kafa kwamatin da zai dakile ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma sauran munanan dabi’u, inda ya bada tabbacin bada goyan baya ga hukumar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: